fidelitybank

Da dumi-dumi: Tsohon shugaban Najeriya ya mutu

Date:

Rahotanni da ke ishe mu cewa, tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya, Cif Ernest Shonekan, ya mutu.

Cif Shonekan ya mutu ne a wani asibiti a birnin Legas ranar Talata, kamar yadda rahotannin suka nuna.

BBC ta rawaito cewa, Tsohon shugaban kasar ya mutu ya na da shekara 89 a duniya.

Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon kwaryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watabn Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.

Dan asalin jihar Ogun, an haifi tsohon shugaban kasar riko na Najeriya a watan Mayun 1936 a Lagos.

Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Lagos daga bisani ya tafi Landan don yin karatun digiri a fannin shari’a. Sannan ya ci gaba da neman ilimi a Jami’ar Harvard.

Ya daɗe yana aiki dsa kamfanin United Africa tun daga shekarar 1964, kuma ya riƙe manyan muƙamai a cikinsa.

Daga baya ya faɗaɗa harkokinsa a kasuwancin ƙasashen waje da kuma shiga harkokin siyasa.

A watan Janairun 1993 ne Cif Shonekan ya zama shugaba kwammitin miƙa mulki a ƙarƙashin shugabancin Janar Ibrahim Babangida.

A lokacin da yake kan mulkin Najeriya, Cif Shonekan ya saki fursunonin siyasa da Janar Babangida ya É—aure.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na É—aukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

ÆŠanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa Æ´an Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa Æ´anbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen Æ™auyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faÉ—a ADC

Tsohon É—an jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

ÆŠan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...
X whatsapp