Wani ma’aikacin majalisar dokokin Najeriya ya fadi ya mutu yayin da ya ke hawa bene na biyu.
Shedun gani da ido sun ce, Abdul Olajide Abayomi, mai shekaru 34, ya gangaro ya fadi a saman matakin benen.
Nan take ya mirgina zuwa matakin saukowa kafin a taimaka masa.
Masu tsaftar muhalli, wadanda suka gan shi lokacin da ya fadi, an ce sun sanar da ma’aikatan da suka kai masa agaji nan take.
rahotanni na cewa, abokan aikinsa sun garzaya da shi asibitin majalisar dokokin kasar, domin kula da lafiyarsa, amma ya mutu a kan hanyar zuwa wurin.
An ce ya mutu ne sakamakon bugun zuciya da wasu cututtukan da ke da nasaba da shi. Ya kasance tare da Sashen Inter-Parliamentary a karkashin Daraktan Inter-Parliamentary da Protocols na ofishin majalisar dokokin kasa.