Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta soke zaben Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dokokin kasa, Ishaku Abbo.
An zabi Abbo ne a watan Fabrairun 2023 a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Kotun kamar yadda gidan Talabijin na Channels ta ruwaito, ta yanke hukuncin ne kan dan takarar jam’iyyar PDP Amos Yohanna.


