Bayan watanni hudu da dakatar da aiki a karshe kamfanin jirigin sama na Dana Air a ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022, ya sanar da cewa zai ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen daga ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta Dana Air ta fitar kuma ta mikawa manema labarai a ranar Juma’a.
Ku tuna cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da Dana Air watanni hudu da suka gabata saboda wasu laifukan da suka saba wa doka.
Sai dai kuma kamfanin jirgin ya ce yana shirin ci gaba da gudanar da harkokin sufurin jiragen sama bayan nasarar kammala tantancewar da NCAA ta shirya.