Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da cewa, wasu fusatattun matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta bayan ya yi garkuwa da ita.
mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa matasan sun kona makarantar ne da tsakar daren ranar Lahadi.
Ya ce“Babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni a lokacin”. In ji SP Kiyawa.
SP Haruna Kiyawa ya kuma kara da cewa, kawo yanzu ba su kama wadanda ake zargi da aikata ta’asar ba.