Tottenham ta fice daga gasar cin kofin Europa Conference, bayan da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA ta kwace mata maki Uku a wasan da ta kauracewa da Rennes.
An dakatar da wasan a ranar 9 ga watan Disamba, sakamakon barkewar cutar Covid, inda a ka samu karin mutane 13 daga kungiyar.
Daga nan Uefa ta ce ba za a iya dage wasan ba, kuma ta mika batun ga hukumar ta ladabtarwa.
Hakan ne ya baiwa kungiyar Rennes nasara da ci 3-0 kuma ita ce ta daya a rukunin, inda Vitesse ta zo ta biyu da Spurs a matsayi na uku.