Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Yobe, Hon. Goni Bukar, ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Damaturu zuwa Kano.
Marigayin wanda aka fi sani da Bugon, kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana, ya rasu ne a daren ranar Talata a hanyarsa ta zuwa jihar Kano.
Tun da farko dai Marigayi Kwamishinan ya halarci sallar jana’izar daya daga cikin mukarrabansa da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe kafin ya wuce Kano.
Marigayi Goni Bukar ya kasance tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Bursari/Geidam/Yunusari a jihar Yobe.
Sojoji biyu da farar hula daya sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a Legas


