A yanzu haka, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na Ƙaramar Hukumar Madobi domin yi wa abokin burmin sa a siyasa, tsohon gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar ƙanin sa, Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.
Jaridar PlatinumPost ta jiyo cewa tuni gwamnan ya isa garin ya kuma yi wa Kwankwaso ta’aziya.
Da fari dai Ganduje ya aikawa Kwankwaso saƙon ta’aziya ne a sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu a jiya Litinin.
PlatinumPost Hausa ta gano cewa a yanzu haka Ganduje na garin na Kwankwaso da ke Madobi domin gudanar da sallar azahar,da ga bisani ya kamo hanya ya dawo Kano.