Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Peter Obi ya mika wuya ga matsin lamba daga kungiyoyin magoya bayansa na neman ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party.
A cewar wani mai fallasa, tsohon gwamnan jihar Anambra yana kammala shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour.
Wannan dai na zuwa ne bayan da jam’iyyar Coalition for Peter Obi (COP), ta matsa wa tsohon gwamnan lamba ya fice daga jam’iyyar PDP domin cimma burinsa na zama shugaban Najeriya. A cewar Naija News.
Kungiyoyin da ke goyon bayan sun gargadi tsohon gwamnan kan abin da zai kasance a fagen siyasarsa idan har ya kasa ficewa daga jam’iyyar PDP, domin yawancin wakilan jam’iyyar ana saye da buhunan kudi da za su kada kuri’a a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai zuwa.