Wasu ‘yan bindiga a yankin sun kashe manoma 12 a ranar Talata a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Mutane uku ne suka samu raunuka yayin harin.
Gakurdi yana unguwar Daddara da tazarar kilomita kadan daga Daddara akan babbar hanyar da ta hada Katsina zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Wani mazaunin garin Daddara, Bashir Salihu a zantawarsa da Leadership, ya ce dukkanin manoman da aka kashe ‘yan garin Gakurdi ne, kuma suna shirya gonakinsu ne gabanin damina.
“Abin da na samu shi ne mazauna yankin sun je share gonakinsu da kuma shirya gonakinsu don fara damina, wanda galibi a lokacin damina ne.
”Ƴan fashin sun je kauyen ne a kan babura, kuma da suka ga manoman, sai suka fara harbi ba kakkautawa. Ban sani ba ko sun shirya kai farmaki kan manoma ko kauyen,” inji shi.
Ya ce ‘yan bindigar ma sun kona wasu gidaje bayan mutanen kauyen sun gudu.
An yi jana’izar wadanda aka kashe a yammacin yau a kauyen.