Kungiyar Kwadago ta ayyana yajin aikin gama gari a fadin kasar baki daya, daga ranar Talata, 14 ga Nuwamba, 2023.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC da Trade Union Congress, TUC ne suka bayyana hakan bayan wani taron gaggawa da suka yi a Abuja ranar Talata.
Idan za a iya tunawa, kungiyar kwadagon ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero, a jihar Imo a makon jiya.


