Kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke, wanda ta tabbatar da sahihancin zaben mazabun da bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC ya gudanar a Kano.
Idan ba a manta ba, a baya ne dai tsagin G7 suka shigar da ƙarar tsagin gwamna Ganduje.
Haka zalika, ko a ranar Alhamis rahotonni na nuni da cewa, Malam Ibrahim Shekarau, ya sasanta da Ganduje tare da ba shi kuejarsa ta sake tsayawa takarar Sanata.