Rahotanni sun tabbatar da cewa, farashin litar man Fetur ya tashi zuwa N617 a birnin tarayya Abuja da safiyar Talata.
Yayin wata ziyara ta musamman gidan man kamfanin mai na ƙasa NNPCL, an tabbatar da cewa kamfanin ya ɗaga farashi daga N539 zuwa N617.
Har yanzun babu sanarwa a hukumance daga mahukunta kan dalilin tashin farashin.
Sai dai a baya yan kasuwa sun yi hasashen farashin litar mai ka iya kai wa N700.