Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya bukaci China ta matsawa Rasha don kawo ƙashen ƴakin Ukraine.
Scholz ya bayyana hakane yayin tattaunawa da shugaba Xi Jinping a Beijing.
Mista Scholz ya ce dukkanin ƙasashen sun amince cewa amfani da makamin nukiliya da Rasha ke ikirari za ta yi abu ne mai hadari.
Shugaban na China, ya ki yin Allah-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Sai dai, ya ce al’ummar duniya su baki wajen ganin an kawo ƙarshen ƴakin cikin hanya mai sauki, a cewar rahotanni daga China.
Ziyarar da Scholz ya kai China ta tayar da hankula a Jamus da wasu bangarori a Turai.