fidelitybank

Chana ta hana ƴan ƙwallon ƙafa yin zane a fatar su 

Date:

 

 

 

Ƙasar Sin, wacce a ka fi sani da China ta hana ƴan ƙwallon ƙafa yi zane a jikin su, wanda a ke kira ‘tatoo’ da turanci.

 

Ƙasar ta kuma umarci wadanda su ka yi zaɓen da su yi maza su goge na jikin su domin tarbiyyar masu tasowa a cikin al’umma, in ji Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar, GAS.

 

Haka kuma umarnin ya haɗa da hukunci ga masu kunnen ƙashi a kan dokar.

 

“An hana ƴan ƙwallon ƙafar ƙungiyar ƙasar nan manya da ƴan ƙasa da shekara 23 yin zane a jikin su,” in ji sanarwar wacce ta fita a ranar Talata.

 

“Waɗanda su ke da shi a jikin su to su yi maza su cire shi. Idan akwai wata matsala, to a rufe wajen a lokacin attisaye ko wasa idan kungiyar ta amince da hakan,”

 

Hakazalika hukumar ta hana ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƴan ƙasa da shekara 20 ɗaukar sabbin ƴan wasa masu zane a jikin su.

 

Rahotanni sun baiyana cewa ba wannan ne karon farko da ƙasar ke harin hana yin zane a jikin su ba.

 

 

 

 

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp