fidelitybank

Buhari ya tafi Gambia rantsar da shugaban kasa

Date:

A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Banjul na kasar Gambia, domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, bayan sake zabensa a karo na biyu.

Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da hakan, a wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yarawaito cewa, Shehu ya ce: “A bisa gayyatar mai masaukin nasa, shugaba Buhari zai kasance babban bako na musamman a wajen bukukuwan da sauran shugabannin Afirka za su halarta a filin wasa na Independence, Bakau.”

Buhari, tare da wasu shugabannin kungiyar ECOWAS, sun taka rawa wajen mayar da mulkin dimokuradiyya a Gambia a shekarar 2017, bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan ya sha kaye a zabe.

Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Amb. Ahmed Rufa’i, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya a karshen bikin rantsar da shi.

 

vangurd 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp