fidelitybank

Buhari ya tafi Gambia rantsar da shugaban kasa

Date:

A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Banjul na kasar Gambia, domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, bayan sake zabensa a karo na biyu.

Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da hakan, a wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN yarawaito cewa, Shehu ya ce: “A bisa gayyatar mai masaukin nasa, shugaba Buhari zai kasance babban bako na musamman a wajen bukukuwan da sauran shugabannin Afirka za su halarta a filin wasa na Independence, Bakau.”

Buhari, tare da wasu shugabannin kungiyar ECOWAS, sun taka rawa wajen mayar da mulkin dimokuradiyya a Gambia a shekarar 2017, bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan ya sha kaye a zabe.

Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Amb. Ahmed Rufa’i, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya a karshen bikin rantsar da shi.

 

the nation newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miÆ™a saÆ™on ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe Æ´an É—aurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin Æ´an Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama Æ´an Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na Æ™asa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta É—aure Matashin da ya shiga É—akin kwanan ÆŠalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp