fidelitybank

Buhari ya mika ta’aziyar sa a kan kisan Hanifa

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa ‘yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyayenta.

Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar a yau Juma’a ta ce Buhari ya ce, yana fatan “hakan zai sa ‘yan ƙasa su ƙara amincewa da ayyukan jami’an tsaro”.

“Shugaba Buhari ya ce iyaye da kuma ‘yan Najeriya da suka dinga bin sawun halin da Hanifa ta shiga sun yi ta fatan za a ceto ta a raye, yana mai cewa aikin gano mutanen da jami’an tsaro suka gudanar da ya kai ga gano gawarta abin a yaba ne…abu ne da ya kamata ya sa mutane su ƙara yarda da mahukunta,” in ji sanarwar.

“In aka samu irin wannan abin alfaharin sai mutane su dinga yabon jami’an tsaro,” a cewar Buhari, wanda ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan ta, sannan ya bai wa iyayenta haƙuri game da “baƙin cikin rashinta”.

A ranar Alhamis ne dai aka gano gawar Hanifa bayan wani malamin makarantarsu ya sace ta a watan Disamba sannan ya kashe tare da binne ta a ɗaya daga cikin gine-ginen makarantar.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp