Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yaba da nasarar da ɗan wasan damben Birtaniya haifaffen Najeriya, Anthony Joshua, ya samu kan abokin karawarsa Jermaine Franklin a karawar da suka yi a filin wasan dambe na O2 Arena da ke birnin London.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita shugaba Buhari ya ce nasarar da Josua ta samu ta nuna cewa ta hanyar aiki tukuru da sadaukarwa da jajircewa ne ake samun nasara.
Shugaban Buhari ya yi fatan nasarar ta kasance ɗaya daga cikin nasarorin da ba za a taɓa mantawa da ita ba a tarihin gasar dambe.
Nasarar ita ce ta 25 da Joshua ya samu, tun bayan zamansa fitaccen ɗan wasan dambe a shekarar 2013. In ji BBC.