fidelitybank

Bugun Zuciya: Kanin Maradona Hugo ya mutu

Date:

Hugo Maradona wanda kanin fitaccen dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego, ya mutu sakamakon bugun zuciya.

Hugo mai shekaru 52 ya fuskanci bugun zuciyar ne a gidansa da ke Naples. Hugo ya mutu da misalin karfe 11.50 na safiyar Talata.

Hakan na zuwa ne watanni 13 kacal bayan da bugun zuciya ya kashe Diego Maradon, gwarzon gasar cin kofin duniya na Argentina kuma daya daga cikin mafi girma da ya taba buga wasan wanda ya mutu a Argentina a watan Nuwamba 2020 ya na da shekaru 60.

Kafin rasuwar Hugo an hango shi filin wasa na Maradona da ke Naples ta kasar Italiya, domin halartar bikin tunawa da dan uwansa marigayi kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa wata daya kacal da ya wuce.

Kafin rasuwar sa ya dai bar mace mai suna Paola Morra, wadda ya aura a shekara ta 2016, tare da ’ya’ya uku.

Ƙananan ‘yan’uwan Maradona da sauran su ne Diego da Raul da Hugo shi ma dan wasan Æ™wallon Æ™afa ne kuma ya sanya hannu tun ya na matsayin matashi ga kungiyar Napoli mai shekaru 18 a 1987.

Amma ba kamar É—an’uwansa ba, wanda ya buga wasa mafi kyawun shekarunsa a Napoli kuma a na girmama shi a birnin Naples ta kasar Italiya a matsayin wani mutum mai daraja.
A ranar 20 ga Satumba, 1987, ‘yan’uwan biyu sun yi wasa da juna tare da Napoli wanda a ka buga 2-1.

Hugo, wanda ya kasance tauraron tawagar Argentina a gasar cin kofin matasa na duniya na FIFA na matasa ‘yan kasa da shekaru 16 a shekarar 1985, wanda ya kasance kan gaba a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, ya ci gaba da taka leda a kananun gasa na Spain da Austria da Venezuela kafin ya kawo karshen aikinsa na buga wasa a Japan a karshen shekarun 1990.

Bayan haka ya koma horarwa, kuma ya shiga cikin ajin manyan makarantun matasa a matsayin masu horaswa.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

ÆŠaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla ÆŠanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An É—age jana’izar Aminu ÆŠantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da É—age jana'izar fitaccen É—ankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp