fidelitybank

Boris Johnson na shan suka mai zafi a majalisar dokokin  Burtaniya

Date:

Gwamnatin Burtaniya na fuskanar tambayoyi cikin gaggawa a majalisar dokokin kasar kan sabbin rahotanni, duk da cewa Johnson da kansa ba zai samu amsa gayyatar ba.

Game da jerin jam’iyyu a titin Downing sun jawo cece-kuce daga shugaban jam’iyyar Labour Keir Starmer, wanda ya ce Johnson ba shi da hurumin jagorantar kasar.

Johnson da abokin aikinsa Carrie suna cikin wadanda suka taru tare da kusan ma’aikata 40 a lambun Downing Street a ranar 20 ga Mayu, 2020, bayan babban sakatare na Firayim Ministan, Martin Reynolds ya aika da gayyata ta imel.

A lokacin taron, an rufe makarantu ga yawancin daliban, kuma an rufe mashaya da gidajen abinci, tare da tsauraran matakai kan cudanya da jama’a. An hana mutane yin bankwana da kai ga ’yan uwa da ke mutuwa.

‘Yan sanda sun gurfanar da mutane da laifin yin liyafa, sun kafa shingayen binciken ababen hawa a wasu yankuna kuma a Derbyshire, tsakiyar Ingila, sun yi amfani da jirage marasa matuka wajen sa ido kan wuraren kyan gani.

Adadin wadanda suka mutu a Burtaniya daga barkewar cutar ta COVID-19 ya kai 150,154, adadin COVID-19 mafi muni na bakwai a duniya bayan Amurka, Brazil, Indiya, Rasha, Mexico da Peru.

‘Yan sandan Landan, wadanda a baya suka ki binciken ikirarin da a ke yi na taron kulle-kulle na jami’an gwamnati, ya ce a ranar Litinin ya na tuntubar ofishin majalisar zartarwa, kan zargin keta dokokin kare lafiya a titin Downing.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...
X whatsapp