fidelitybank

BON: Badaru ya gargadi gidajen rediyo da talabijin

Date:

Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya ce, wajibi ne kafafen yada labarai na rediyo da talabijin su samarwa da kansu mafita, sakamakon yadda wasu kafafen sada zumunta ke yada labarai na kanzon kurege.

Badaru ya tabbatar da hakan ne yayin taron kaddamar da kwamitin kungiyar kafafen yada labara shiyar Arewa maso Yamma wanda ya gudana a ranar Laraba a Dutse.

Yayin taron shugaban kwamitin hukumar kula da kafafen yada labarai na jihar Jigawa, Alhaji Mati Ali, wanda ya kasance a matsayin mai saukar baki a taron, ya ja hankalin gidajen rediyo da talabijin da su kara zage damtse a kan ayyukan su.

Dr Bello Sule ya gabatar da mukala mai taken ”Kalubalen da kafafen yada labarai ke fuskanta daga kafafen sada zumunta tare da damar da a ke da ita’.

Ya ce”Babbar illar da ke tattare da harkar yada labarai a yanzu shi ne, marasa ilimi ne su ka dabaibaye harkar wanda ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen yada labarai da hotuna marasa tushe balle makama a cikin al’umma”.

Taron ya samu halartar shugabannin wasu kafafen gidajen rediyo da na talabijin da ke yankin Arewa maso Yamma.

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...
X whatsapp