fidelitybank

Boko Haram sun kai hari tare da yin garkuwa da jami’an ‘yan sanda

Date:

‘Yan kungiyar ta’adda ta Boko Haram sun kai farmaki makarantar horas da ‘yan sanda ta Mobile da ke karamar hukumar Limankara Gwoza a jihar Borno, inda suka yi awon gaba da mutane da dama.

Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito, masu garkuwan sun tafi da wasu ‘yan sandan na Mobile wadanda ba a tantance adadinsu ba.

Makarantar horarwa ta na kilomita ashirin da biyar daga garin Gwoza, mahaifar Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sojoji. Gari ne mai iyaka tsakanin Borno da karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce mayakan ‘yan tada kayar bayan sun kai hari makarantar horon ne a daren ranar Alhamis da manyan bindigogi inda suka rinka harbin iska kafin su yi awon gaba da jami’i mai bayar da umarni.

Harin dai na zuwa ne kwanaki bakwai, bayan da ‘yan ta’addan suka yi yunkurin kutsawa cikin sansanin sojojin Najeriya da ke Gwoza inda wasu sojojin Najeriya suka yi nasarar fatattakar su.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume ya kai ziyarar aiki zuwa rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin kwanaki biyu da suka gabata.

Har ila yau, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya koka da yadda matsalar tsaro a jihar da kuma yankin Arewa maso Yamma ke ciki a halin yanzu, inda ya bukaci sojoji da su daina sassauta musu.

A cewar Zulum, ‘yan ta’addan Boko Haram a yanzu suna bukukuwan aure, suna karbar haraji daga wasu al’ummomi ba tare da wata arangama da sojoji ba.

legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp