fidelitybank

Biyan Bashi: Babu batun sayar da kadarorin Najeriya – Ofishin Kula Bashi

Date:

Ofishin kula da basussuka na Najeriya (DMO) ya ce, ba ya cikin yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kasar Sin na cewa za ta jinginar da wasu kadarorinta ko da ta gaza biyan bashinta.

Babbar daraktar Ofishin, Misis Patience Oniha ce, ta sanar da hakan yayin tattaunawarta da kamfanin dillancin labarai na NAN a Abuja ranar Asabar.

A cewar ta,”Babu wata yarjejeniyar jinginar da wasu kadarorin gwamnatin Najeriya a cikin bashin, bashin da kasar Sin ke bin Najeriya bai wuce Dalar Amurka biliyan 3.59 ba, wanda ke zaman kaso 9.4 cikin 100 na Dala biliyan 37.9 din da ta ciyo daga ketare. Ya zuwa karshen watan Satumban 2021, jimlar bashin da ake bin Najeriya shi ne biliyan 37.9, wanda ya kunshi wanda gwamnatin tarayya da jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya su ka ciyo daga ketare. Amma jimlar bashin da aka ciyo daga Sin bai wuce kaso 9.4 cikin 100 b, basussukan kuma ba sa bukatar wata jinginar kadara a matsayin sharadi, kawai yarjejeniya ce”. Inji Misis Patience.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai a ka ta ce-ce-kuce a kafafen sada zumunta da na yada labarai cewa, wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya na fuskantar barazanar karbe wasu muhimman kadarorinsu daga kasar Sin, saboda bashin da kasar ke bin su.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp