Sojojin ruwa na ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo da Najeriya sun ƙaddamar da shirin “Operation Safe Domain II” mai taken ‘ƙarfafa tsaro a bakin teku ta hanyar haɗin gwiwa don cigaban yankuna’.
An gudanar da taron ne a ranar Litinin a Jamhuriyar Benin.
Sai dai jamhuriyar Nijar daya daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ba ta halarci taron ba.
A cewar daraktan cibiyar haɗin kan tekun da ke shiyyar E, Kwamado Aniedi Ibok, aikin wani ɓangare ne na yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya wa hannu a shekarar 2014.
Ibok ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta bai wa sojojin ruwa na kowace ƙasa damar yaƙi da masu aikata laifuka ba tare da takaita iyaka ba


