Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta batun tattaunawar sulhu da a ka ce ya na yi da Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Aminiya ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata hira ta musamman da a ka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, inda ya ce. ya ji dadin ziyarar ta’aziyyar da Gwamnan ya kai masa ta rasuwar kaninsa.
Sai dai ya kore yiwuwar bawa Ganduje damar samun wani matsayi ko mukami idan damar hakan ta samu ta bangarensa.
Ya ce “A yanzu dai ka san ba a jam’iyya daya mu ke ba, domin haka ina ganin babu ma bukatar yin wannan tambaya, domin haka ko da dama ta samu akwai mutanen da suka cancanta cikin wadanda na ke tare da su”.
A makon da ya wuce Kwankwaso ya musanta rade-radin da a ke na cewar ya na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP tare da shirin sauya sheka zuwa APC, wanda hakan ya zama batun tattaunawa na tsawon lokaci a kafafen watsa labarai.
Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya yi tsamari tun bayan 2015 bayan Gwamnan Kano na yanzu ya dare kan kujerar mulkin Jihar.
Sai dai a baya-bayan Ganduje ya nuna cewar akwai yiwuwar yin sulhu da tsohon uban gidan nasa a siyasa, wanda ya ce tun asali wasu ne suka shiga tsakaninsu.
Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta APC tsakaninsa da tsagin tawagar tsohon Gwamna kuma Sanatan Kano ta tsakiya a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau.
Wanda a ke rikicin shugabancin jam’iyya tsakanin, Abdullahi Abbas da Haruna Abdullahi Zago.