fidelitybank

Duban talakawa za su ci gaba da zaman gida saboda rufe makarantu – Mazauna Zamfara

Date:

Yayin da a ka koma makarantu a faɗin Najeriya a ranar Litinin, wasu iyayen yara a jihar Zamfara sun koka a kan rashin buɗe makarantun su.

Mazauna yankin sun ce rashin komawa makarantun ‘ya’yansu a safiyar yau, alama ce da ke nuna cewa dubban ‘ya’yan talakawa a jihar za su ci gaba da zaman gida tsawon zangon karatu na biyu ke nan.

Gwamnatin Zamfara dai ta rufe makarantun jihar ne a farkon watan Satumba, bayan sace gomman ɗalibai daga Sakandiren Ƙaya a cikin ƙaramar hukumar Muradun da yammacin ranar wata Laraba.

Wani mahaifi ya shaida wa BBC cewa suna tsaka mai wuya; ”Mu na kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta duba girman Allah ta bude mana makarantun yara, wannan matsalar tsaro wadda ita ce a ka ce ta janyo rufe makarantun ba wai Zamfara kadai ta shafa ba, shin don me a nan za a mayar tamkar nan ne gidan matsalar”.

An yi zango guda yara na zaman gida, yanzu duk inda za a koma makaranta ban da namu ‘ya’yan. Kowancan Term guda da aka yi wasu daga cikin mutanenmu da sun san ba za a koma makarantar ba da tuni sun dauki mataki,” in ji shi.

An dai rufe makarantu tun watan Agustan bara, watanni biyar kenan, kuma babu wata magana guda har ya zuwa yanzu na bude makarantun.

 

 

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa ƴar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar Ɗangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp