fidelitybank

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Date:

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana haka ne a matsayin martani ga gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ƴanƙasarta da ke birnin Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Watsa Labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, inda a ciki ya ce, “gwamnatin Najeriya ta samu labarin gargaɗin da Amurka ta aika wa ma’aikatan ofishin jakadancinta da ma ƴanƙasarta da ke Abuja game da tsaro.

“Duk da gwamnatin Najeriya na girmama haƙƙin da ofisoshin jakadanci – ciki har da na Amurka – ke da shi na ba ƴanƙasarta shawara ko gargaɗi game da matsalolin tsaro, yana da muhimmanci mu tabbatar da cewa babu wata barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta, sannan mazauna birnin da masu ziyara babu wata barazana da suke fuskanta.”

Sanarwar ta ƙara da cewa akwai cikakken tsaro a Abuja, “domin jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da daƙile dukkan wata barazanar tsaro.”

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...
X whatsapp