Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato Mohammed Babangida ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya ƙi amincewa da muƙamin da shugaba Bola Tinubu ya naɗa shi.
An dai ta yaɗa wata takarda, wadda a ciki ake cewa Mohammed ya ce ba ya son naɗin da aka masa na shugabantar kwamitin gudanarwa na bankin noma na ƙasar.
A jawabinsa na ƙaryata batun, Mohammed ya ce, “ban ajiye muƙamin ba aka naɗa ni ba. Takardar da ake yaɗawa ta bogi ce, kuma aikin masu neman tayar da zaune tsaye ne.
“A shirye nake in yi aiki da shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin noma domin bunƙasa ɓangaren noma da samar da abinci a Najeriya.”
A makon jiya ne dai gwamnatin Tinubu ta sanar da naɗa Mohammed Babangida a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin noma na ƙasar a cikin wasu jerin naɗa-naɗe da gwamnatin ta yi.