fidelitybank

Ba za mu yarda a sanya wa Trump anƙwa ba a hannu – Lauya

Date:

Lauyan tsohon shugaban Amurka ya ce ba za a sanya wa Donald Trump ankwa ba, idan ya halarci zaman kotu a New York a makon gobe.

An tambaye shi ne a gidan talbijin na ABC News ko yaya yake zaton tsarin gurfanar da Trump gaban kotu zai kasance, Joe Tacopina ya ce ya “tabbata [masu shigar da ƙara] za su yi ƙoƙarin samun duk wani ɗigo na jan hankalin jama’a da za su iya, a kan wannan abu.

Amma ya ƙara cewa ba za a sa wa shugaban ankwa ba”.

Tun farko rahotanni sun tabbatar da Za a iya kama Donald Trump nan da ƴan kwanaki. Lauyan Trump ya ce: “Na fahimci cewa za su rufe hanyoyin zuwa yankin da ke zagaye da kotun, idan an zo gurfanar da shi, kuma su rufe ginin kotun. In ji BBC.

“Za mu je can… kuma mu ce ba a aikata laifi ba, za a fara magana ne game da hanyar shigar ƙararrakin, abin da za mu yi kenan nan take kuma ba tare da ƙaƙƙautawa ba, dangane da dacewar wannan ƙara ta fuskar shari’a.”

Kotu a birnin New York ce, ta tuhumi tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da hannu kan zargin biyan kuɗi domin ɓoye alaƙar da ke tsakaninsa da wata mai fina-finan batsa.

Ana zargin Trump ne da biyan kuɗi ga matar mai suna Stormy Daniels gabanin zaɓen 2016 domin ta rufe baki kan alaƙar da ta wanzu tsakaninsu

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...
X whatsapp