Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta ce ƙasar “ba za ta taɓa yarda a fitar da Falasɗinawa daga Gaza ba, ko Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ko datse Gaza, ko kuma sauya iyakar zirin na Gaza”.
Kalaman nata na zuwa ne yayin ganawarta da Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, inda ta gode masa bisa rawar da yake takawa wajen kwashe ‘yan Amurka daga Gaza.
Yayin tattaunawar tasu a Dubai, a gefen taron COP28, Harris ta ce za a cimma abin da aka saka a gaba ne kawai “idan aka bi su ta hanyar lumana a fayyace wajen sama wa Falasɗinawa ƙasarsu ta kansu ƙarƙashin Hukumar Falasɗinawa [Palestinian Authority]”.
Harris ta kuma bayyana ƙarara cewa Hamas ba za ta sake mulkin Gaza ba kuma Amurka za ta “dage wajen ganin an sako dukkan mutanen da Hamas ɗin ke garkuwa da su a Gaza”.


