fidelitybank

Ba za mu amince da karin kudin jinya a AKTH ba – JOHESU

Date:

Wata taƙaddama da ta taso tsakanin gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU da shugabancin asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, na barazana ga dumbin marasa lafiya a jihar Kano.

Takaddamar ta taso ne kan karin kudi a ɓangarori daban-daban da shugabancin asibitin ya yi, abin da kungiyar ta ce, ba za ta saɓu ba, saboda hakan zai ƙara jefa jama’a cikin matsi.

An shiga wannan tirka-tirka ce tsakanin gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya reshen asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sakamakon zargin cewa shugaban asibitin, ya ninka kudin asibiti, sannan JOHESU suka zarge shi da sayar da wasu bangarori na asibitin.

A baya-bayan nan cikin matakan da kungiyar ta dauka kan wannan al’amarin, har da barazanar cewa matukar lamarin ya ci gaba nan da 21 da daya ga wannan watan, to za ta shiga yajin aiki.

Wannan matakin dai ana ganin zai iya kara jefa dumbin marasa lafiya cikin kunchi.

To sai dai shugaban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abdu Sheshe, da ke karkashin Jami’ar Bayero, ya ce batun gina wasu wurare a asibitin, ana yi ne karkashin shirin hadin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa wanda gwamnatin tarayya ke ba da damar a yi.

Farfesa Abdurrhaman ya ce za su zauna da mambobin kungiyar domin tattauna yadda za a shawo kan wannan al’amari, nan gaba cikin wannan mako.

Bayanai na cewa daruruwan marasa lafiya ne ke ziyartar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano a kullum, wadanda suke cike da burin ganin an sasanta wannan takaddama don kaucewa shiga mawuyacin hali. In ji BBC.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...
X whatsapp