A cikin daren jiya shugaban kasar Ukraine ya wallafa wani bidiyo cikin wadanda yake wallafawa a kullum. Sai dai a wannan karon ya wallafa shi ne daga ofishin shugaban kasa da ke birnin Kyiv.
Ya ce, ba boyewa yake yi ba. Kuma ya ce, ba ya tsoron makomarksa.
A na ganin bayyana wurin da ya ke ga duniya sako ne ga Vladimir Putin, domin har yanzu dakarun Ukraine na kare birnin Kyiv daga harin da Rasha ke kai wa kan babban birnin kasar na Ukraine.