Jam’iyyar Labour, LP ta ce, ba ta cikin duk wata tada zaune tsaye na shirin kafa gwamnatin wucin gadi.
Wannan shine a cewar mai magana da yawun jam’iyyar adawa, Yunusa Tanko, yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, ranar Alhamis.
Shugaban jam’iyyar ya fayyace cewa jam’iyyar ba ta da hannu a cikin shirin kafa gwamnatin wucin gadi ga ‘yan Najeriya.
Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta tabbatar da wani shiri na zagon kasa ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya.
Sai dai a martanin da DSS ta yi, Tanko ya ce jam’iyyar LP za ta ci gaba da tsayawa kan tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya don kare ‘yan Najeriya.
“Ba mu cikin duk wani shiri na tayar da kayar baya ko kadan.
“Amma abin da nake cewa shi ne, za mu kare muradun al’ummar Najeriya ne bisa tanadin doka, wadda ta tanadi cewa inda kuke cutar da ku, kuna da ‘yancin yin zanga-zanga kuma za ku yi hakan tare da kariya da kare lafiyar ku. jami’an tsaron Najeriya. Abin da za mu yi ke nan, amma ba za mu goyi bayan duk wani tayar da kayar baya ba ta kowace hanya.”