Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta kammala shirin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano.
Jam’iyyar ta yanke wannan shawarar ne bayan dan takararta na gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a ranar Laraba, ya taya zababben gwamna, Engr. Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), jim kadan bayan ya samu takardar shedar lashe zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Amma Kakakin Jam’iyyar APC a Kano, Ahmed Aruwa, a ranar Asabar, ya yi nuni da cewa, jam’iyyar ta umurci tawagar lauyoyin ta da su fara gudanar da shari’a, inda suke kalubalantar sakamakon zaben da ya baiwa dan takarar gwamnan NNPP nasara, kamar yadda INEC ta bayyana.
Ya ce APC ta Kano na tuhumar NNPP, dan takararta na gwamna, da INEC.
Karanta Wannan: A dakata da baiwa gwamnatin Kano bashi – Abba
A cewarsa, “Jam’iyyar APC ta Kano ta yi watsi da sakamakon da INEC ta bayyana, wanda ya tabbatar da dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.”
Ya kara da cewa ayyana wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya sabawa dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.
Aruwa ya bayyana cewa, shugabannin jam’iyyar na jihar sun umarci hukumar da ta ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da ke zamanta a harabar kotun Miller.
A cewarsa, duk da cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Gawuna, ya taya zababben gwamnan murna, “Jam’iyyar APC na da yakinin cewa wannan shelar ya saba wa dokokin zabe da aka shimfida, wanda ya sa APC ta yanke shawarar ci gaba domin neman hakkin shari’a a gaban kotu mai hurumin da ya dace”.