Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar APC ya amince da sake fasalin jadawalin ayyuka na zabukan fidda gwanin da za a gudanar a babban zaben shekarar 2023.
Jam’iyyar APC a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, ta amince da sauya jadawalin zaben gwamnoni, ‘yan majalisar jiha, majalisar dattawa da ta wakilai,” in ji kakakin APC.
Mista Morka ya bayyana cewa, za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamna, wakilan jiha, majalisar dokoki, da na kananan hukumomi a ranar 26 ga Mayu.
Ya bayyana cewa, za a gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa da na kananan hukumomi a ranar 27 ga watan Mayu, yayin da ‘yan majalisar wakilai da na kananan hukumomi za su gudanar da zaben fidda gwani a ranar 28 ga watan Mayu.
Ya sake jaddada cewa, za a gudanar da babban taron jam’iyyar na musamman na zaben fidda gwani na shugaban kasa na shekarar 2023 kamar yadda aka tsara, a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu.
“Babban taro na musamman na zaben fidda gwani na shugaban kasa kamar yadda aka tsara daga ranar Lahadi, 29 ga Mayu zuwa Litinin, 30 ga Mayu,” in ji Mista Morka.