Gabanin zaben shugaban kasa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za ta iya yin kasa a gwiwa ba a zaben 2023.
Ta kuma bukaci mata da matasa na jam’iyyar APC da su yi gangamin zagaye da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima.
Ta yi wannan kiran ne a wata ganawar sirri da uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Remi Tinubu da matan gwamnonin APC a ranar Lahadi a Abuja.
Ta ce: “An kafa kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na mata da matasa na APC Tinubu/Shettima don tsara hanyoyin yakin neman zaben 2023. Don haka ina neman hadin kan ku wajen kai jam’iyyarmu ga nasara.
“Gobe, za a kaddamar da tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na mata da matasa na jam’iyyar APC domin hada kai da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa don zaburar da goyon bayan jam’iyyarmu mai daraja.
“Muna dogara gare ku da ku dage da wannan yunkuri a matsayin babban majibincin tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na mata da matasa.
“Ba za mu iya yin rashin nasara ba, amma mu yi aiki tare a matsayin babban karfi don cimma nasara a zaben 2023. Jam’iyyar APC ta zabi ‘yan takararta a dukkan kujerun siyasa. Yanzu lokaci ya yi da za mu sake farfado da harkar mu.”