fidelitybank

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Date:

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra’ila, don adawa da matakin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa farmakin sojin da take a Gaza.

A ranar Juma’a ne majalisar tsaron Isra’ila ta amince da sharuɗa biyar na kawo karshen yaƙin, ciki har da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, inda sojojin Isra’ilar suka ce za su “shirya karɓe iko” da birnin Gaza.

Masu zanga-zangar da suka haɗa da iyalan mutum 50 ɗin da ake garkuwa da su a Gaza – ciki har da 20 ɗin da ake kyautata zaton suna raye, suna fargabar cewa shirin zai saka rayuwar ƴan uwansu cikin haɗari, inda suka buƙaci gwamnatin Isra’ila da ta yi ƙoƙarin don ganin an sake su.

Shugabannin Isra’ila sun yi watsi da sukar da ake yi wa shirinsu, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce “hakan zai taimaka a saki mutanen mu”.

Wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan waɗanda ake garkuwa da su ta wallafa a shafin X cewa: “Faɗaɗa farmakin zai saka mutanen mu da kuma sojoji cikin barazana – al’ummar Isra’ila ba su da niyyar saka su cikin haɗari”.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp