fidelitybank

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Date:

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra’ila, don adawa da matakin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa farmakin sojin da take a Gaza.

A ranar Juma’a ne majalisar tsaron Isra’ila ta amince da sharuɗa biyar na kawo karshen yaƙin, ciki har da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, inda sojojin Isra’ilar suka ce za su “shirya karɓe iko” da birnin Gaza.

Masu zanga-zangar da suka haɗa da iyalan mutum 50 ɗin da ake garkuwa da su a Gaza – ciki har da 20 ɗin da ake kyautata zaton suna raye, suna fargabar cewa shirin zai saka rayuwar ƴan uwansu cikin haɗari, inda suka buƙaci gwamnatin Isra’ila da ta yi ƙoƙarin don ganin an sake su.

Shugabannin Isra’ila sun yi watsi da sukar da ake yi wa shirinsu, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce “hakan zai taimaka a saki mutanen mu”.

Wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan waɗanda ake garkuwa da su ta wallafa a shafin X cewa: “Faɗaɗa farmakin zai saka mutanen mu da kuma sojoji cikin barazana – al’ummar Isra’ila ba su da niyyar saka su cikin haɗari”.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari a ƙauyuka 15 na Zamfara a mako ɗaya – Rahoto

Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle...

Jihohin Arewa huɗu ne suke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 – NUP

Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce...

A karon farko an gurfanar da Mutanen da ake zargi da kai hari Cocin Owo

Mutum biyar da ake zargi da shirya harin bam...

Peter Obi na nan a cikin jam’iyyar har yanzu – LP

Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce...

Yadda Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje a Filato

Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar...

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra'ila,...

Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da suka aikata laifi zuwa kasarsu

Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk...

NDLEA ta kama Fasto kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Gwamnoni sun mika sakon ta’azziya ga iyalan Audu Ogbeh

Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu...

Duk wahala sai dai mu mutu a Gaza – Fatma

Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce, duk runtsi...

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...
X whatsapp