fidelitybank

An tono gawar wani Almajiri bayan an binne shi a Kano

Date:

Gwamnatin jihar Kano, ta bayar da umarnin tono gawar wani almajiri wanda ake zargin malaminsa ya halaka shi ta hanyar duka.

Kwamishinan Harkokin Addinai Dr. Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci bankado makarantar ’yan marin da ke unguwar Wailari a yankin Na’ibawa.

Aminiya ta rawaito cewa, ana zargin malamin da yi wa almajirin dukan kawo wuka, lamarin da ya yi ajalinsa.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa lokacin da almajirin ya rasu ba a sanar da iyayensa ba aka je aka binne shi.

Baba Impossible ya bayyana cewa, gwamnatin ta sa ’yan sanda su hako gawar almajirin tare da gudanar da bincike, domin gano musabbabin rasuwarsa.

Da yake nasa jawabin, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa a yanzu haka mai makarantar da sauran wadanda ke taimaka masa suna hannu, domin fadada bincike a kai tare da rufe makarantar.

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp