An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na ƴan China da ke Bye pass titin Naʼibawa zuwa Hotoro a Kano.
Rahotonnin da Arewa Updates ta samu sun nuna cewa alʼamarin ya faru ne da safiyar Asabar 21 Yuni, 2025.
Wani da ke aiki a wajen ya ce, tuni jamiʼan yan sanda suka killace wajen inda aka garzaya da wadanda abin ya shafa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.
Masu aikin ceto na ci gaba da aiki a wajen.