Alkalin alkalan jihar Borno, Mai Shari’a Kashim Zannah, ya rantsar da alkalan Shari’ar Musulunci 21 a jihar.
Da yake magana a taron rantsarwar ranar Talatan nan a birnin Maiduguri, Mai Shari’a Zannah ya bukaci sababbin alkalan da su jajirce wajen gudanar da aikinsu kamar yadda suka dauki rantsuwar kama aiki.
Ya kuma yi kira da su gudanar da shari’o’in da za a gabatar musu bisa turbar doka da rantsuwar da suka dauka.
Ya ce “Kowannenku ya zo ne saboda cancanta ba don wani iko ba ko hanya, saboda haka ba za ku wahala wajen fahimtar mu da muke cewa ba za mu amince da cin hanci da rashawa ba. Babu yadda za a yi mu amince da cin hanci da rashawa.
“Za mu hukunta duk mutumin da aka samu da cin hanci ta korarsa daga aiki da tozarta shi. Wannan shi ne kadai hukuncin, ba rage matsayi ba ko sauyin wajen aiki. Babu wata mafita a wannan lamari, kamar yadda ba mu da mafita wajen zaben ku wannan aiki saboda kun ci jarrabawa.’


