fidelitybank

An kuma ƙwata wa: Tankar mai ta yi bindiga yayin da ƴan ganima su ka mamaye ta

Date:

Ana fargabar mutane da yawa sun rasu wasu kuma sun ji rauni yayin da suke kokarin dibar man fetur daga wata tankar mai da ta fadi a kwanar Dikko da ke, babban titin Abuja zuwa Kaduna, a jihar Naija.

Rahotanni na cewa lamarin wanda ya faru yau Asabar, ya kasance ne lokacin da tankar da ke gudu ta fadi man ya zube, mutane suka je suna kwasar man sai motar ta yi bindiga wuta ta tashi.

Wutar ta kone mutane da dama da ke kwasar man yayin da wadanda suke nesa da ita kuwa suka ji rauni.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Bologi Ibrahim, wanda shi ne kakakin gwamnan jihar ta Naija, Mohammed Bago, wanda ke cikin tawagar gwamnan da ke kan hanyarta ta zuwa Suleja da Tafa domin duba ayyuka, ya tabbatar mata da aukuwar lamarin.

Kakakin ya ce gwamnan ya nuna alhininsa a kan hadarin sannan ya bayar da umarni ga jami’an tsaro su tabbatar da tsaro a wajen sannan dukkanin hukumomin gwamnatin jihar su yi abin da ya wajaba a kai.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp