fidelitybank

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Date:

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace shanu a wani sabon rikici da ya ɓarke a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau.

Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata amfanin gona da sace shanu da kashe wasu dabbobin, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels a ƙasar ya ruwaito.

Cikin wata sanarwa da rundunar soji ta ‘Operation Safe Haven’ ta fitar ta ce rikicin ya fara ne tun a ranar Litinin 12 ga watan Mayun da muke ciki, a lokacin da aka zargi wasu fusatattun matasa da kashe wasu shanu da suka yi zargin sun shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar ta Riyom.

A ranar 13 ga watan ne kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Danchindo domin ramuwar gayya, tare da kashe mutum huɗu kafin su tsare bayan zuwan jami’an tsaro.

Haka kuma a ranar 14 aka zargi wasu mahara da kashe dabbobi 26 tare da raunata wasu a garin Darwat.

Daga baya kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Wereng Kam tare da kashe mutum shida.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...
X whatsapp