fidelitybank

An kashe ƴan Boko Haram biyar a Borno

Date:

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile wani harin Boko Haram a ƙauyen Warambe na karamar hukumar Gwoza na jihar Borno, inda suka hallaka mayaƙa biyar.

Warambe ɗaya ne daga cikin ƙauyukan da ke ɗauke da mutanen da aka sake mayarwa yankin, inda ƴan ta da ƙayar baya suka sha yin yunkurin afka wa ƙauyen.

Shugaban maharban yankin, wanda ya tabbatarwa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce mayaƙan ƙungiyar sun yi wa ƙauyen tsinke ne da misalin karfe shida na yammacin ranar Juma’a.

“Sai dai sun gamu da jami’an mu inda aka yi artabu har ta kai ga biyar daga cikin ƴan ƙungiyar suka kwanta dama. Mun ƙwato makamai da harsasai waɗanda ke yanzu haka ke karkashin ikon sojoji,” in ji shi.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp