fidelitybank

An karawa ma’aikata albashi kwatankwacin kudin Najeriya Naira 137,500

Date:

Kasar Turkiyya ta sanar da yi wa ma’aikatanta karin albashi da kaso 50 cikin 100 a daidai lokacin da ta ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma karyewar kudin kasarta,

Shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan, wanda ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce karin shi ne irinsa mafi girma a tarihin kasar cikin shekara 50.Kuma karin dai na nufin yanzu mafi karancin albashi a kasar zai kai kudin kasar na Lira 4,250, kwatankwacin Naira 137,500, sabanin Lira 2,826 (N91,000) da ake biya a baya.

Bugu da kari, karin albashin zai shafi kimanin ma’aikata miliyan shida a kasar.

Erdogan ya ce, “Mun himmatu wajen rage wa mutane halin rashin tabbas din da suka fada sakamakon tashin gwauron zabon da kayayyaki suka yi, da kuma ci gaba da karyewar darajar kudin kasarmu.”

Shugaban ya kuma sanar da cewa kasar za ta dauke wa ’yan kasar biyan wasu kudaden haraji daga cikin sabon albashin.

Tattalin arzikin kasar Turkiyya dai na shan fama da kalubale, ta inda sai da darajar kudin kasar ta ragu da kusan rabi, in aka kwatanta ta da Dalar Amurka tun farkon watan Janairun bana. Inji Aminiya.

Alkaluman hauhawar farashin dai ya haura kaso 21 cikin 100 wanda Babban Bankin Kasar ya yi harsashe.

Sai dai jam’iyyun adawa a kasar na harsashen ta yiwu alkaluman ma sun wuce haka.

 

dailysun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp