fidelitybank

An damƙe ƴan Shi’a 19 a Abuja

Date:

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja, sun tabbatar da kama mambobin kungiyar ƴan shi’a 19 kan gudanar da zanga-zanga ba tare da izini ba.

A cikin wata sanarwa da ta samu a hannun mai magana da yawun ƴan sandan, SP Josephine Adeh, ta ce mambobin kungiyar sama da 400 sun fito zanga-zanga daga Babbar Kotun Tarayya zuwa dandalin Eagle Square.

Sanarwar ta ce bayan fitowarsu sun kuma toshe hanyoyi bayan hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da bukatar bai wa jagoran kugiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky fasfo din sa.

Karanta Wannan: An cafke ƴan fashi da makami 14 a Kano

El-Zakzaky ne ya shigar da ƙarar Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, inda ya bukaci ta sake masa fasfo ɗin sa da na matarsa da ta ƙwace.

Sai dai da yake yanke hukunci, mai shari’a Obiora Egwuatu, ya ce El-zakzaky ya kasa gabatar da hujjoji da suka nuna cewa DSS ɗin ta karɓe masa fasfo bayan dawowarsa daga Indiya.

Josephine ta ce mmbobin kungiyar sun yi ta jifa da duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari kan ƴan sanda, amma daga bisani aka samu damar tarwatsa su tare da kama 19 daga ciki waɗanda ta ce za a kai su kotu.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...
X whatsapp