Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Litinin, ta gurfanar da wani matashi dan shekara 17 mai suna Abdulrahman Ibrahim, bisa zargin kashe wani dillalin waya a cikin birnin Katsina.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, CSP Gambo Isah, ‘yan sandan sun samu nasarar cafke wanda ake zargin ne bayan da ya jawo dilalin wayar a cikin wani gini da bai kammala ba a unguwar Modoji, Katsina, ya kuma daba masa wuka a wuyansa, inda daga karshe ya mutu.
Abdulrahman Ibrahim a wata hira da manema labarai yayi zargin cewa ya kashe mutumin ne domin kare kansa.
A cewarsa, “Na kashe shi ne a lokacin da yake so ya kashe ni kuma ya raunata ni a hannu.”
A wani labarin kuma, CSP Gambo ya ce jami’an ‘yan sanda na rundunar sun kai samame a wasu maboyar ‘yan ta’adda a cikin babban birnin jihar, inda suka kama wasu mutane 72 da ake zargin barayin jama’a ne, wanda aka fi sani da Kauraye a kasar Hausa da wata dabara ta satar waya.
A cewar CSP Gambo, yankunan da aka kai samame sun hada da: Sabuwar Unguwa, Gadar Nayalli, Modoji, Tudun YanLihida, Kwabren Dorawa, Janbango, Abbatuwa, Filin Canada, Lambun Dankwai, Kofar Marusa, Tsalawa, da Chake da dai sauransu.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana jin dadin ta ga jama’a kan yadda suke ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ‘yan uwa mata a jihar baki daya, inda ta bukace su da su rika kai rahoton duk wani mutum ko wata kungiya da suka samu matsala ga ‘yan sanda ta wadannan layukan gaggawa kamar haka: 08156977777, 09053872247.


