fidelitybank

An cafke ƴan fashi da makami 14 a Kano

Date:

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta kama mutum 14 waɗanda take zargi da aikata fashi da makami da tu’ammali da ƙwayoyi da kuma aikata dabanci a makon farko na watan azumin Ramadan.

Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.

Ta ce ta kuma ƙwato muggan maƙamai da haramtattun ƙwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.

A wata sanarwa da kakakin runduar ƴan sanda jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau’i na aikin dabanci a faɗin jihar.

Karanta Wannan: Ƴan Sanda sun kaddamar da yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƴan Dana a Kano

Ƴan sandan sun ce suna iyaƙar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan ɓata-gari a jihar.

CP Mamman Dauda ya gargaɗi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.

Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...
X whatsapp