Yan sanda sun ce, sun kama mutum 17 bisa zargin laifuka daban-daban ciki har da tashe-tashen hankula bayan zaɓe, da fashin daji da satar shanu da kuma sara suka a jihar Zamfara.
A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce jami’ansu sun yi kamen ne a sassa daban-daban na Zamfara, tare da ƙwato muhimman kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargi.
Karanta Wannan: Buhari ya jinjina wa Ɗan Dambe Joshua
Rundunar ta ce daga cikin mutanen da ta kama har da wani fitaccen ɗan fashin daji wanda ya addabi jihar mai suna Sulaiman Balarabe, ɗan shekara 25.
Ta kuma ce ta kama ɗan fashin dajin – wanda da ma sunansa ke cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa-a-jallo – ranar Laraba 29 ga watan Maris
Bayan kama wanda ake zargin ne kuma, ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa yana da hannu a hare-hare da sace mutane don neman kuɗin fansa.
Haka zalika a cewar sanarwar ‘yan sanda, Sulaiman Balarabe ya ce ya karɓi miliyoyin kuɗaɗee daga hannun imakusantan da ya sace wa ‘yan’uwansu.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce ta kama ƙarin mutum uku bisa zargin satar shanu da sauran ƙananan dabbobi, a lokacin da suke kan hanyar zuwa Gusau daga Dansadau, da dabbobin a cikin motoci guda biyu.
Sanarwar ta ambato kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, CP Kolo Yusuf na yaba wa al’ummar jihar bisa haɗin kai da suke bai wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ya sake jaddada kiransa ga Zamfarawa su ci gaba da bai wa jami’an tsaron goyon baya don tabbatar da ganin kwanciyar hankali da zaman lafiya sun dawwama a jihar.